Runadunar yan sandan Jihar Nassarawa ta bayyana cewa shugaban karamar hukamar Keffi Mahammad Shehu Baba ya shaki iskar yanci tare da mataimakamasa a jiya Asabar.

ÀSP Rahman Nansel mai magana da yawun rundunar shine ya bayyana haka ga jarida News agency a yau Lahadi.

Ya ce an samu nasarar ne sakamakon matsawar da hukumomin tsaro da jami ai suka yi

Shugaban karamar hukumar Shehu Baba tare da maitaimakamasa an yi garkuwa da su a ranar Juma’a da kuma hallaka jami in dan sanda Alhassan Habib akan babbar hanyar Keffi zuwa Akwanga.

Mai magana da yawun rundunar ta yan sandan ya ce Mahammad ya shaki iskar yanci da maitaimakamasa a daren jiya Asabar da misalin karfe 9:00 PM na dare, sannan an samu nasarar kama wadanda ake zargi mutum Uku a kusa da kauyen Gitttata a karamar hukamar Keffi.

Yan bindigan sun zo ne daga yankin Jihar Kaduna domin gudanar da shirin karbar kudin fansa

Leave a Reply

%d bloggers like this: