Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, ta ce ɗage lokutan zaɓukan fitar da gwani da jam’iyyun siyasa ke yi idan an bar su zai yi mummunar illa ga zaɓe shekarar 2023 na kasar nan.

Rotimi Lawrence Oyekanmi, babban sakataren yaɗa labarai na shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya sanar da hakan a ranar Lahadi a Abuja cewa INEC ta bai wa jam’iyyu isasshen lokaci domin yin zaɓen fitar da gwani.

Yayin martani, Oyekanmi ya ce:

“INEC tana da ƙarfin ikon bada lokacin zaɓen fitar da gwani, akasin yadda wasu ke kallo.

A bayyane yake bai karanta dokokin zaɓe ba wanda hakan abun kunya ne.

“A lokuta daban-daban har uku, shugaban INEC ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da su yi zaɓen fitar da gwaninsu a cikin lokacin da jadawali ya nuna saboda ba za a sake tsawaita lokaci ba.

“Idan aka amince da ƙarin lokacin, hakan zai lalata tsarin shirin zaɓen 2023 wanda hakan zai tabbatar da babbar illa.

“Me yasa jam’iyyun ba za su yi zaɓen fitar da gwani ba cikin watanni biyu da aka tsara.?

Abun mamaki, babu wanda ya yi ƙorafin kan jadawalin lokacin da INEC ta fitar a watan Fabrairu. Me yasa sai yanzu?” Ya tuhuma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: