A ranar Lahadin da ta gabata mayakan IPOB sun hallaka wata mata mai juna biyu, yaranta 4 da kuma wasu mutane 6, waɗanda duk ƴan arewa ne da ke zama a Jihar Anambra.

Sun halaka matar, wacce ke ɗauke da juna biyu da yaranta ne a anguwar Isulo, dake karamar hukumar Orumba ta Arewa a jihar.

Kashe-kashen wani sabon salon ta’addanci ne da yan IPOB su ke kan yi wa waɗanda ba asalin ƴan jihar ba, kuma har sojoji da ƴan sanda ba su bari ba.

Hatta asalin ƴan Jihar Anambara da kuma ƴan yankin Kudu maso Gabas ba su kyale ba, saboda burinsu na kafa kasar Biafra.

Sai dai bayan sa’o’i 48 da kashe-kashen ranar Lahadi wanda aka dinga halaka ƴan arewa ba tare da sun yi komai ba, babu wata jarida ko gidan talabijin da su ka wallafa labarin duk da yadda hotunan su ka bazu a kafafen sada zumunta da kuma caccakar da jami’an tsaro, ƙungiyoyi da mutane su ka dinga yi.

Kashe-kashen ƴan arewan da ƙungiyar, mai keta dokoki ta yi ya auku ne bayan kwanaki kaɗan da bayyanar ɗan majalisar Jihar Anambra wanda ƴan ta’adda su ka sace.

Sarkin Hausawan ƙaramar hukumar Orunba ta arewa, a jiya ya koka akan harin, inda ya ce ƴan arewa mazauna Jihar Anambra sun yanke shawarar barinta saboda yadda mambobin Ƙungiyar Tsaron Gabas (ESN) ta mayakan IPOB a kullum su ke halaka musu ƴan uwa.

A tattaunawar da ya yi da manema labarai Muhammad, ya ce halaka matar mai juna biyu da yaranta huɗu ba sabon abu ba ne a wurinsu saboda an daɗe ana halaka musu mutane ta irin wannan salon.

Ya ci gaba da cewa:

“Matar asali ƴar Jihar Adamawa ce. Kafin rasuwarta, ta zauna a Orumba ta Kudu ne kuma a ranar Lahadi ta je kai wa wasu kawayenta ziyara ne tare da yaranta huɗu.

“A hanyarta ta komawa gida aka halaka ta. An daukota a babur ɗin haya, daga nan ƴan bindigan su ka kai musu farmaki, su ka halaka ta da yaranta huɗu yayin da mai babur ɗin ya tsere.”

A wani bidiyo wanda ke yawo a kafar sadarwa ta Twitter, wadanda aka halaka su na kwance a ƙasa cikin jini, jikinsu duk harsashi, sai aka ji wani ya na magana da harshen Ibo ya na cewa: “Kowa ya kalli wannan bidiyon, sun harbi wata mata da yaranta hudu.

Duk ƴan arewa ne, harbin duk wanda su ka gani a hanya su ke yi; don haka kowa ya kula.”

Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Alhamis ɗin sun halaka ƴan acaba biyar sannan sun babbake baburansu a karamar hukumar Onocha.

An kai gawawwakin huɗu daga cikinsu ma’adanar gawa yayin da su ka babbaka gawar ɗaya.

A cikin kwanakin karshen mako an babbake wata babbar mota wacce ta shiga Kudu da kaya yayin da aka halaka direban da wasu.

Yanzu haka direbobin manyan motoci da ke kudu maso gabas sun ce a tsorace su ke harkoki a yankin.

A ranar Litinin, Kwamishinan ƴan sandan jihar, Echeng E. Echeng ta zargi mazauna jihar da rufa wa masu laifin asiri.

Ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai akan kisan ɗan majalisar Jihar Anambra, Okechukwu Okoye da hadiminsa, Cyril Chiegboka.

Mayakan IPOB sun lashi takobin ci gaba da halaka ƴan majalisar Jihar Anambra. Ya ce ana kiran masu laifi da ƴan bindigan da ba a san su ba, alhalin akwai waɗanda su ka san su. Kuma akwai jami’an tsaron da ke rufa asirin masu laifin wanda hakan ba daidai ba ne.

Leave a Reply

%d bloggers like this: