Rahotonni daga birnin tarayya Abuja, sun bayyana cewa jami’an ƴan sanda sun yi harbe-harbe sararin samaniya a gidan tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha domin tarwatsa masu zanga-zangar adawa da kama shi.

BBC ta ruwaito cewa, masu zanga-zangar mutane ne da ke cin gajiyar tsohon gwamnan don haka suke yunƙurin hana cafke shi.

Jami’an hukumar ƴan Sanda dana EFCC sun shiga gidan Rochas, din da niyar kamashi.

Tun da fari jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC da jami’an ƴan sanda, sun buƙaci manema labarai dasu bar gidan.

A yau ne jami’an EFCC, suka yi dirar mikiya a gidan Rochas Okorocha, domin kama shi bisa ƙin amsa gayyatar da suka yi masa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: