Gwamnatin Tarayya, a ranar Talata, ta ce za ta kashe Naira miliyan 999 a kullum don ciyar da ɗalibai kusan miliyan 10 a shirin ciyar da makarantu na ƙasa a faɗin ƙasar nan.

Shugabar ƙungiyar NHGSFP, Aishatu Digil, ta bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki kan hanyoyin raba ku6daden don duba farashin ciyar da abinci a cikin shirin a Abuja.
Ta ce ministar agajin jin kai da kula da bala’o’i da ci gaban al’umma Sadiya Farouq ta samu amincewar kashe Naira 100 ga kowane mutum a kullum wajen ciyar da shirin.

Ta ce ɗalibai 9,990,862 daga firamare aji ɗaya zuwa uku a shirin yanzu za a ciyar da su da N100 a kullum na tsawon kwanaki 20 a cikin wata da6ya, wanda zai kai Naira miliyan 999,086,200 a kullum.

“Kafin wannan, muna ciyar da yaran makaranta Naira 70 ga kowane yaro, kowane abinci.
Hakan ya kasance tun 2016, amma Shugaban ƙasa ya amince da N100 na sake dubawa.
“Muna da dukkan masu ruwa da tsaki kamar Hukumar Abinci ta Duniya, Hukumar Ƙididdiga ta ƙasa, Hukumar Wayar da kan Jama’a ta ƙasa , Global Alliance for In Proved Nutrition, Ma’aikatun Noma, Ilimi da sauran su don yin shawarwari kan yadda za a raba kuɗaɗen.