Tsohon Sanata kuma ɗan takarar gwamna, Shehu Sani, ya soki sakamakon zaɓen fidda gwani na gwamna da jam’iyyar PDP ta gudanar a jihar Kaduna.

Sani ya yi zargin cewa cin hanci da rashawa ne ya karkata akalar zaɓen inda wakilai ke karɓar kuɗi domin kaɗa ƙuri’ar waɗanda ba su cancanta ba.

Ya ce, “Babu bambanci tsakanin ƴan fashi da ke karɓar kuɗin fansa da wakilai masu karɓar kuɗi don kaɗa ƙuri’a.”

Sani dai ya sha alwashin ba zai ba wa wakilai cin hanci domin su zaɓe shi ba.

“Babu wanda ya isa ya biya kowane wakili a madadina. Ban yi imani da al’adun siyasa na biyan kuɗi don zaɓe ba.

A gabanin zaɓen ranar Laraba, Sani ya ce
Hakan bai dace da aƙida na ba.

Sani wanda ya samu ƙuri’u biyu kacal ya sha kaye a hannun tsohon ɗan majalisar wakilai Isah Ashiru a takarar neman tikitin takarar gwamna a jam’iyyar PDP.

Leave a Reply

%d bloggers like this: