An yanke wa wani rago hukuncin daurin shekaru uku a gidan gyaran hali bayan an rahoto cewa ya tunkuri wata mata hakan kuma ya yi sanadin mutuwarta.

Ragon ya kai wa Adhieu Chaping, mai shekaru 45 hari, ya tunkure ta a kirji sau da dama kafin daga bisani ta rasu a karshen makon da ya gabata.

A cikin hukuncin da aka yanke masa, ragon zai shafe shekaru uku a daure a wani barikin sojoji bayan masu sarautun gargajiya a Sudan sun yanke masa hukunci kamar yadda News Week ta rahoto.

Wannan hukuncin na zuwa ne bayan mai ragon ya amince zai biya iyalan mamaciyar diyya da shanu guda biyar.

Hukumomi sun tabbatar da cewa iyalan mamaciyar sun yarda a basu shanu biyar bayan masu sarautan gargagiya sun shiga tsakani.

A cewar wani jami’i a unguwar mai suna Paul Adhong Majak, masu ragon yan uwan mamaciyar ne kuma makwabta ne.

An rahoto cewa za a mika ragon ga iyalan Chaping bayan ya kammala zaman gidan yarin.

Iyalan biyu sun ratabba hannu kan yarjejeniyar amincewa da hakan da yan sanda da mutanen gari a matsayin shaidu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: