Shugaban kasa Muhammad Buhari ya sanarwa da gwamnonin jam’iyyar su ta APC cewa shine wanda zai tsayar da dan takarar shugabancin Najeriya a shekarar 2023 mai kamawa.
Shugaban ya bayyana hakan ne a jiya Talata a taron ganawa da ya yi da gwamnonin a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja.
A yayin taron shugaba Buhari ya bayyana wa gwamnonin cewa hadin kansu da goyan bayan su ya ke nema ga duk wanda ya tsayar.
Shugaban Buhari ya bukaci shugabannin jam’iyyar da gwamnonin da su dunkule guri daya domin ganin an fitar da dan takarar.
Shugaban ya kuma shaida musu cewa dukkan wadanda jam’iyyar za ta fitar a matsayin dan takara to mutum mai nagarta da kishin talakawan sa.


