Fitaccen malamin addinin musulunci a Najeriya Sheik Ahmad Gumi ya shawarci gwamnatin ƙasar da ta samar da hukumar domin kula da matsalolin fulani.

Mlamin ya ce akwai buƙatar samar da hukuma da za ta dinga lura da matsalolin Fulani kamar yadda aka yi wa mutanen yankin Neja-Delta.

Shiek Gumi ya bayar da shawarar ne a yayin wani taron Fulani da aka shirya a kan tsaro wanda ya gudana a babban birnin tarayya Abuja ranar Laraba.

Taron da aka yi domin duba halin tsaro wanda ƙungiyar fulani makiyaya da wasu ƙungiyoyin su ka halarta a Abuja.

Malamin ya ce abin da ya fi kamata gwamnatin Najeriya ta yi shi ne ta mayar da hankali wajen kawo ƙarshen matsalar fulani ta hanyar samar da ma’aikata ko hukumar da za ta dinga fuskantar matsalolinsu kansacewar a kowanne lokaci fulanin na kokawa da matsalar gwamnati.

Ƙungiyoyin fulanin sun ce akwai abin dubawa a kan yadda satar mutane ta zama ruwan dare kuma daga cikin waɗanda abin ya shafa akwai fulani kasancewar har da su ake hallakawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: