Rundunar yan sandan Jihar Nassarawa ta tabbatar da kubutar yayan tsohon shugaban hukumar ƙidaya a Najeriya NPC daga hannun yan bindiga ajiya Laraba.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Rahman Nansel ya bayyana haka ga manema labarai a jiya Laraba.

A ranar Lahadin da ta gabata ne yan bindiga su ka farma gidan Alhaji Umaru kigbu a unguwar Azuba Bishayi karamar hukamar Lafiya inda su ka hallaka shi tare garkuwa da yayan sa biyu mata.

Rahman Nansel ya ce wadanda aka yi garkuwa da su din sun kubuta ne sakamakon matsin lamba da jami’an yan sanda su ka yi.

Sannan wadanda aka yi garkuwa da su an hada su da iyalin su bayan binciken lafiyar su da aka yi a babban asibitin Dalhatu Araf.

Da muka tutubeshi ko sai da aka biya kuɗon fansa? ya ce bai sani ko an biya kudi ko ba a biya ba kafin sakin su.

Sai dai bayan tutubar iyalan wadanda aka yi garkuwa da su sun ce, sai da su ka biya Naira Miliyan 30 kafin sakin yan uwan na su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: