Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta fara bincike domin lalubo hanyoyin da za a samar da sauƙin kayyakin masarufi a faɗin ƙasar.

Ministar kuɗi da kasafi a Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed ce ta bayyana haka a yayin wani taron majalisar ƙoli ta ƙasa da aka gudanar a Abuja.

Ministar ta ce su na kan aiki cikin gaggawa domin kawo ƙarshen tsadar kayan abinci daa ke fama da shi a ƙasar.

Ta ƙara da cewa gwamnatin ta ɗauki wasu matakai domin haɓaka wasu masana’antu masu ƙarfi a ƙasar musamman waɗanda su ke fusknatar matsala.

Gwamnatin na shirin shirya wani taro na ƙasa tare da ganawa da masu ruwa da tsaki don ganin an shawo kan matsalar.

A cewar ministar nan ba da jimawa ba gwamnatin za ta sanar da sabbin tsare-tsare domin shawo kan matsalar da ake fuskanta na matsin tattalin arziƙi da tsadar rayuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: