Wani matashi a jihar Kano ya sadaukar da shaidar kammala yi wa ƙasa hidima ga Sanata Rabi’u Kwankwaso.

Matashin mai suna Mu’az Mu’azzam Yunusa ya da ya karɓi sakamakon kammala yi wa ƙasa hidima ya yanke shawarar sadaukar da sakamakon nasa ga Sanata Kwankwaso a wani ɓangare na bayar da gudunmawarsa.


Matashin ya ce ya yi hakan ne ganin yadda Sanata Kwankwaso ke mayar da hankali wajen ganin ƴan jihar Kano sun yi karatu.
Mu’az Mu’azzam ya ce ya daɗe ya na sha’awar tsarin gudanar da tafiyar siyasar Kwankwaso musamman yadda ya ke nuna damuwa ga karatun ƴaƴan talakawa.
Ya ce kishin jihar Kano nee ya sanya matashin ya sadaukar da sakamakon kammala yi wa ƙasa hidima don bayar da gudunmawarsa ga siyasar Kwankwaso.