Daga Khadija ahmad Tahir

Jami’an tsaron hadin gwiwa na MNJTF na kasa da kasa sun hallaka mayakan Boko Haram da ISWAP 805 a lokacin da su ke gudanar da atisaye don kawo karshen ‘yan ta’addan.

Jami’an tsaron sun fara atisayen ne tun a watan maris din shekarar 2022.

MNJTF ta bayyana cewa ta samu nasarar ne sakamakon sabbin dabarun yaki don ganin an kawo karshe mayakan.

Kwamandan hukumar Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim ne ya bayyana hakan inda ya ce daga cikin jama’an tsaron da su ka gudanar da atisayen sun hada sojin ruwa sojin sama da kuma sojin kasa.

Janar Khalifa ya bayyana hakan ne a hedkwatar hukumar da ke zaman ta N’Djamena a kasar ta Chadi,inda ya ce sun yi hakan ne domin fatattakar mayakan daga sansanonin su da ke kusa da yankin Tafkin kasar Chadi.

A yayin jawabin sa janar Khalifa ya ce hakan da su ka yi ya kawo sauye-sauye masu tarin yawa a guraren da su ka kaddamar da ayyukan na su wanda kuma mazauna yankunan su ka koma yankunansu bayan faruwar lamarin.

Ibrahim Khalifa ya kara da cewa sama da mayaka 4,000 ne su ka mika wuya sannan su ka kubtar da sama da mutane 3,000 daga hannun mayakan kuma su ka hallaka mayakan 805.

Leave a Reply

%d bloggers like this: