Akalla mutane 5 aka yi garkuwa da su tare da kone motoci 4 wanda ake zargin mayakan kungiyar ISWAP ne su ka kai hari karamar hukamar Kaga a Jihar Borno.

Maharan sun kai harin ne da misalin karfe 10 na safe tsakanin Minok da Jakana a jiya Litinin.
Mutane biyar da ake zargin mayakan sun sace amma an samu nasarar cetosu a cewar hukumomi tsaro Jihar Borno.

A cewar hukumomi tsaron, yan bindiga sun kone motoci hudu a kan babbar hanyar Goni Matari zuwa Minok da jakana.

A halin yanzu yankin yana cikin kulawar jami an tsaron hadin gwiwa bayan tarwasta yan ISWAP zuwa daji.
Sai dai wani dan sa kai mai suna Musty Baballe mazaunin garin Minok ya ce kafin maharan su sakawa ababen hawan wuta sai da su ka sace kayan abincin motocin.
Babale ya ce da zuwan mayakan ISWAP fasinjojin motocin su ka shiga daji domin tsira da rayuwar su tare da barin motocin a kan babbar hanya.