Wasu da ake zargi ƴan bindiga ne sun hallaka mutane shida a daren Laraba wayewar Alhamis.

Ƴan bindigan sun kashe mutanen nen a unguwar Sabo kuma ake kyauta zaton mutanen da aka hallaka Hausawa ne.

Rahotanni sun tabbatar da cewar ƴan bindigan sun jikkata mutane da dama a harin da su ka kai bayan mutane shida da su ka mutu.

Maharan sun kai harin ne haye a kan babura sannan su ka buɗewa mutanen wuta.

Jami’an tsaro a jihar sun tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai sun ce ɓarayi ne su ka kai harin ba ƴan bindiga ba kamar yadda mai magana da yawun ƴan sandan jihar ta bayyana.

Wannan harin na zuwa ne ƙasa da awanni 72 da wasu ƴan bindiga su ka kai wani mummunan hari wata coci a Owo.

Tuni jami’an tsaro su ka ce sun fara bincike domin zaƙulo maharan da masu hannu a kai harin domin fuskantar hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: