Ƴan bindigan da suka yi awon gaba da Mai unguwan Rijana, Ayuba Dodo Dakolo, sun sake shi bayan an biyan kudin fansa.

Ayuba Dodo Dakolo ya samu ‘yanci ne a ranar Litinin tare da mutum biyu da aka yi garkuwa da su.

‘Yan uwan mutanen sub bayar da kudi, babura, wayoyin salula kafin su iya ceto su.

Daya daga cikin dan uwan wadanda aka dauke ya bayar da labarin abin da ya faru, sai dai ya takaita maganarsa domin ‘yan bindiga sun ja kunnensu kan magana da ‘yan jarida.

An dauke Ayuba Dodo Dakolo ne a gonarsa da ke wani kauye da ake kira Kurmi a kusa da garin Chikwale, karamar hukumar Kachia, Kaduna.

Daga cikin abubuwan da masu garkuwa da mutanen suka bukata daga ‘yanuwan basaraken har da babura, fetur, man juye, tayoyi, sigari da katin waya.

‘Yan uwan waɗanda aka sae sun kai dukkanin kayan da ƴan bindigan su ka buƙata kafin sakin mutanen.

Dakolo ya tabbatar da cewar ya kubuta daga hannun ‘yan bindigan sannan yace sai da ya saida bangaren gonarsa kafin ya iya biyan kudin fansa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: