Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta ƙara kayan aikin yin rijistar katin zaɓe na din-din-din a wasu jihohin Najeriya.

wannan na zuwa ne yayin da mutane ke ci gaba da nuna sha’awar yin rijistar katin zaɓe don tinkarar zaɓen shejarar 2023.
Hukumar ta ƙara na’urar yin rijistar guda 209 a jihohin Kano, Legas, da wasu jihohi biyar a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Kwamishinan zaɓe na ƙasa kuma shugaban kwamotin wayar da kan jama’a a kan muhimmancin katin zaɓe Festus Okoye ne ya bayyana haka yau Asabar.

Matakin hakan ya zo ne bayan da mutane da dama ke ci gaba da ƙorafi a kan rashin wadatar kayan aikin rijistar kuma hakan ya sa ba su yi ba har lokacin da wa’adin ya cika.
Hukumar zaɓe ta gudanar da wani zama a Abuja ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu kuma ya gana da kwamishinonin zaɓe na jihohi 36 na Najeriya.
Zaman ya duba halin da ake ciki tare da duba ƙorabin al’umma a dangane da katin zaɓen.
Hukumar ta ce ta bayar da wannan damar kuma za ta ci gaba da sa ido a kai domin ganin ci gaban da za a samu a kai.