Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu fastoci uku a kan hanyar Ochadamu-Okele-Ejule a ranar Juma’a a karamar hukumar Ofu ta jihar, inda suka bukaci a biya su N80m domin samun ‘yancinsu.

Daily Trust gano cewa daya daga cikin malaman da aka sace Fasto Sunday Emmanuel Abbah a karamar hukumar Olamaboro yake, amma yana zaune a Lokoja.

Fastocin uku an ce suna kan hanyarsu ne daga Lokoja domin yin addu’a a wani shiri na kwanaki 3 zasu gabatar na ’yan ta’adda a wani yanki da ke Gabashin Jihar Kogi a lokacin da maharan suka kaddamar wa motarsu a kusa da garin Ochadamu-Okele-Ejule tare da kai su daji.

Wata majiya daga iyalan daya daga cikin fastocin da aka sace ta ce masu garkuwar sun yi kira da a biya su N80m kafin a sako fastocin.

Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da faruwar lamarin na garkuwa da mutane, inda ta ce ta tura jami’anta zuwa yankunan domin ganin an sako mutanen.

A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP William Aya, “Rundunar ta na sane kuma tana kokarin ganin an sake su”.

Leave a Reply

%d bloggers like this: