Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a yau Lahadi, 12 ga watan Yuni, ya nuna damuwa kan matsalar rashin tsaro a kasar Najeriya.

Buhari ya kuma roki yan Najeriya da su dage da addu’a a kan ranshin tsaro a cikin jawabinsa na ranar Damokradiyya ta 2022 da ya yiwa yan kasar a Abuja.

A cewarsa, gwamnatin tana aiki tukuru domin magance matsalolin tsaro a kasar nan.

Ya ce “a kullum ina rayuwa cikin bakin ciki da damuwa saboda matsalar tsaro”.

“Don cimma wannan, dole sai dukkanmu mun bayar da gudunmawa, ba aiki gwamnati bane ita kadai, Ina bukatar dukkanin al’ummar kasar da su taimaka sannan su ba hukumomin tsaronmu hadin kai ta hanyar kai rahoton duk wani abun da basu yarda da shi ba ga hukumomin tsaro.”

“A wannan rana ta musamman, ina so dukkanmu mu sanya wadanda ayyukan ta’addanci ya ritsa da su a zukatanmu da addu’o’inmu.

A kullum ina rayuwa cikin bakin ciki da damuwa saboda wadannan mutane da wadanda ke garkame sakamakon ta’addanci da garkuwa da mutane.

Ni da hukumomin tsaro muna yin duk mai yiwuwa don kubutar da wadannan maza da matan cikin koshin lafiya.

Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta gyara wasu tsare-tsaren tsaro na kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: