Aƙalla mutane 15 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu suka ɓace a safiyar Lahadi bayan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari ƙauyen Igama a Edumoga Ehaje ta ƙaramar hukumar Okpokwu ta jihar Benue.

Maharan da su ka kai harin sun je da yawansu kuma sun kone gidaje da dama a yankin.

A yayin da aka tuntubi shugabar karamar hukumar, Amina Audu, ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce ba su gano dalilin kai harin ba.

Shugabar karamar hukumar wacce tace ta je ofishin ‘yan sandan Okpoga domin duba gawawwakin wadanda aka halaka, ta ce an kai gawa tara ma’adanar gawawwaki yayin da ake cigaba da neman sauran.

Amina Audu ta koka kan harin sannan ta sanar da cewa makiyaya dauke da makamai ne suka shiga yankin da yawansu.

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin kuma sai dai ta ce ba ta samu cikakken bayanin babban jami’in da ke kula da yankin ba..

Leave a Reply

%d bloggers like this: