Shugaban hafsoshin tsaro na Najeriya Janar Lucky Irabor, ya ce sojoji sun daƙile wani shirin ‘yan da ‘yan ta’adda na kai hari wasu birane a Najeriya.

Janar Lucky Irabor, ya ce ‘yan ta’adda sun shirya kai wasu hare-hare a Abuja da wasu manyan biranen a makon da ya gabata.

Duk da an hallaka mutane 40 a wata coci da ke garin Owo a jihar Ondo, babban hafsan sojin ya ce ba don namijin kokarinsu ba, da ta’adin ya zarce haka.

Janar Irabor ya ce ‘yan ta’adda sun shirya kai makamancin harin a jihar Kano sai dai sun yi nasarar hana faruwar hakan.

Babban hafsan sojin ya bayyana haka ne yayin da aka yi hira da shi a wani shiri da aka yi a kan ranar damukaradiyya a gidan talabiji na Channels TV ranar Lahadi.

Rundunar sojin ta bayyana yadda su ka bankado mugun nufin da ‘yan ta’adan ke yi tare da gano wasu kayyaki na haɗa bama-bamai.

Janar Irabor ya ce sun gano tulin makamai da harsashi da wasu kayan da ‘yan ta’adda suka nemi su yi amfani da su a wasu yankin kasar ciki har da birnin Abuja.

Duk da kashe-kashen da ake fama da shi, babban jami’in sojan ya ce ana samun ci gaba a harkar tsaro a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: