Rundunar tsaro a Najeriya ta gagaɗi ƴan siyasa a kan abubuwan da ka iya haifar da tarzoma.

Babban hafsan tsaron Najeriya Janar Lucky Irabo ne ya bayyana haka a yayin ganawa da ƴan jarida a Abuja.
Lucky Irabo ya ce wajibi ne ƴan siyasa su mutunta duk wata doka da ƙasa ta samar domin tabbatar da zaman lafiya.

Ya ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya hori jami’an tsarro da su tabbatar da tsaro a yayin da ake tunkarara zaɓen shekarar 2023.

Janar Irabo ya ce wajibi ne yan siyasa su kaucewa furta kalaman tunziri, ko wata hanya da ka iya haifar da fitina a Najeriya.