ɗan takarar shugaban ƙasa a babbar jam’iyyar dawa a Najeriya PDP Atiku Abubakar ya zaɓi gwamnan jihar Delta a matsayinw anda zai masa mataimakin shugaban ƙasa.

Atiku Abubakar ya bayyana ɗaukar Ifeanyi Okowa a matsayin wanda zai yi masa mataimakin shugaban ƙasa a babban zaɓen shekrar 2023 mai zuwa.
hakan ya faru a yau Alhamis a Abuja yayin taron ƙarshe domin bayyana mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP bayan kammala tantancewa.

Atiku Abubakar ya ce akwai buƙatar zaɓen wanda ya cik sharuɗan da ake buƙata wanda hakan zai taimaka musu wajen cin nasara a zaɓe na gaba.

Ya ce jam’iyyar PDP na buƙatar samun wanda ya ke da sani a kan tattalin arziƙi ta yadda zai taimaka mata wajen damun nasara a bisa abubuwan da su ka tunkara.
Sauran jam’iyyu na duba yiwuwar ɗaukar mataimakin shjugaban ƙasa kafin wa’adin da hukumar zaɓe ta sanya wanda ya ke cika a gobe Juma’a.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta sanya ranar 17 ga watan da mu ke ciki a matsayin ranar da ta sanyawa jam’iyyun ƙasar don miƙa sunayen ƴan takara shugaban ƙasa da mataimakansu.