Wata guguwa da mamakon ruwan sama sun yi sanadin rasuwar mutum daya sannan ta rushe gidaje 32 a kauyen ’Yan Tsagai da ke Karamar Hukumar Rano ta Jihar Kano.

Shugaban Hukumar bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) Dokta Sale Jili ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Alhamis.

Ya ce mutane da dama sun rasa muhallinsu, wanda hakan ya sanya wasunsu neman matsuguni a gidajen makwabta da ’yan uwa.

Dakta Jili ya kuma ce hukumar ta tura ma’aikatanta zuwa kauyen domin ragewa mutane radadin asarar da hakan ya jawo musu.

Ya ƙara da cewa sun ziyarci kauyen Tsagai kuma sun raba tallafi ga wadanda lamarin ya ritsa da su.

Daga cikin kayan tallafin da su ka bayar akwai buhunan shinkafa 30, na masara 30, sai buhun wake 30, na siminti 30 da kuma kwanon rufi da kusoshi.

Sauran kayayyakin da hukumar ta ce ta raba sun hada da botikan roba da cokula da man gyada da katifu da tumatirin gwangwani da kuma sinadaran dandanon girki.

Jili ya shawarci al’ummar yankin da su dinga kula da gyara magudanun ruwansu da shara, tare da gargadinsu kan gina gidaje a kan magudanun ruwa domin gujewa aukuwar makamancin lamarin a gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: