Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta cire sunan shugaban majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan daga cikin sunayen ‘yan takarar da kuma wasu mutane biyu da su ke neman takara a zabe mai zuwa.

Bayan cire sunan Ahmad Lawan hukumar ta cire sunan gwamnan Jihar Ebonyi Dave Umahi da kuma ministan Neja Delta sanata Godwill Akpabio wanda kafin zaben fidda gwani su ka tsaya takarar shugaban kasa a jamm’iyyar APC.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a a hukUmar ta INEC shine ya sanar da cire sunayen ‘yan takara da hukumar ta fitar a jiya Juma’a.

Kwamishinan ya bayyana cewa idan jam’iyya ta mikawa hukumar zabe sunan wani dan takara wanda ba ta hanyar zaben fidda gwani aka zabe shi ba to babu shakka hukumar ba za ta sanya sunan sa a cikin ‘yan takara ba.

Ya kara da cewa dukkan wanda hukumar zabe ta ambato sunan sa a jiya juma’a to ba ta hanyar zaben fitar da gwani aka zabe shi ba.

Sannan ya ce babu wata doka da ta tilasta wa hukumar zaben ta sanya sunan wani dan takara da ba a zabeshi ta hanyar zaben fidda gwani ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: