Kwamandan rundunar ‘yan banga na jihar Neja, Nasiru Mohammed Manta, ya bayar da umarnin rufe dukkan ofisoshin hukumar da ke fadin jihar.
Hakan ya biyo bayan kama shi tare da tsare shi da ‘yan sanda suka yi bisa umarnin kwamishinan ‘yan sandan, Monday Bala Kuryas.
Manta ya shaida cewa an kama shi ne sakamakon kama wasu ɓata gari da suka addabi mutane da rashin zaman lafiya a Minna babban birnin jihar.
Ya yi zargin cewa iyayen wasu ɓata gari ne da ya kama suka kai shi ga kwamishinan yan sanda wanda ya bayar da umarnin tsare shi bayan sun yi ci zarafinsa a bainar jama’a.
Manta ya ce, bayan daukar su da gwamnatin jihar ta yi, ba a biya su albashi ba amma har yanzu suna aikinsu.
Ya ce a cikinsu babu wanda ke samun albashi, Kuma duk lokacin da suka kama bata gari suna mika su ga ’yan sanda, ba wai suna daukan mataki da kan su ba.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da lamarin.
Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Emmanuel Umar, a watan Disambar shekarar da ta gabata, ya ce gwamna Abubakar Sani Bello ya amince da dokar ‘yan banga ne domin bunkasa ayyukan rundunar da kuma karfafa tsaro a jihar.