Akalla mutane 158 cutar zazzabin lasa ta hallaka a jihohi 24 a fadin kasa Najeriya cikin watanni shida na shekarar 2022 da mu je ciki.

Hukumar da ke aikin dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya NCDC ita ce ta bayyana haka a jiya Litinin.
Ta ce mutanen da cutar ta kama sun fito ne daga kananan hukumomi 99 na kasar.

Sannan cutar tafi kama yan shekaru 21 zuwa 30 har ma zuwa masu shekara 90.

Hukumar ta ce mutane 158 sun mutu sakamakon cutar Lassa wanda hakan ke nuna karuwar cutar.
Sannan yawan waɗanda aka kara samu da cutar a wannan lokaci ya fi hauhawa a Jihohin Ondo Edo da kuma Filato.
Kuma ba a samu wani ma’akacin lafiya ba daya kamu da cutar kamar yadda aka saba samu a baya ba.
Hukumar NCDC ta ce suna nan suna aiki da ma’akatar national fever lassa multi patner domin kawo karshen cutar a kasa baki daya.