Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC reshen jihar Kano ta ce ta fara aikin faɗaɗa hanyoyin rage cunkoso tare da tabbatar da cewar ƴan jihar Kano da su ka kai shekaru 18 zuwa sama sun mallaki katin zaɓensu na dindindin.

Shugaban hukumar farfesa Riskuwa Arabu Shehu ne ya bayyana haka yau a helkwatar hukumar yayin taron manema labarai.

Ya ce duba ga yawan mutane da su ke zuwa domin yin rijistar zaɓe, akwai buƙatar faɗaɗawa domin rage cunkoso tare da samar da ƙarin na’u’rorin rijistar ta yadda za a sauƙaƙwa jama’a.

Daga cikin ayyukan da hukumar ta mayar da hankali a kai akwai gyara ga waɗanda katin zaɓensu ya samu matsala ko ya lalace ko kuma ya ɓata, da waɗanda su ka samu sauyin gari ko unguwa ko mazaɓa, sai mutanen da su ka kai shekaru 18 kuma ba su taɓa yin rijistar kartin zaɓe ba.

Haka kuma hukumar ta jadda cewar mutanen da su ke da rijistar zaɓen, babu buƙatar su sabuntata muddin ba matsala ne katin ya ke da shi ba.

Farfesa Riskuwa Arabu Shehu ya ce hukumar ta duƙufa wajen ganin an ci gaba da aikin rijistar zaɓen a filin wasa na Sani Abacha indoor stadium da ke unguwar ƙofar mata a Kano.

Sannan hakan ba zai shafi sauran wuraren da ake yin rijistar ba kamar ofisoshin hukumar na ƙananan hukumomi da ma helkwatar hukumar da ake gudanar da katin zaɓen a hain yanzu.

Ya ƙara da cewa akwai wasu jami;an hukumar da za su dinga shiga mazaɓu domin yin rijistar katin zaɓen ga waɗanda ba su da shi ko gyara ga masu matsala.

Haka kuma hukumar ta ja kunnen masu ƙoƙarin sabunta rijistar da gangan a kan cewar, akwai doka da aka tanada ta ɗauri ko tara ko kuma a hadawa mutum biyun muddin aka sameshi da laifin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: