A kalla rayuka 17 sun salwanta bayan wadanda suka samu matsanantan raunuka yayin da ‘yan ta’adda suka kai farmaki mahakar ma’adanan da ‘yan kasar Sin ke kula dashi tsakanin Ajata da Aboki cikin gundumar Gurmana na karamar hukumar Shiroro da ke jihar Neja.

An ruwaito yadda harin ya auku ranar Laraba da tsakar rana inda aka halaka mutane 17 duk da ‘yan sandan da ke tsere mahaka ma’adanan da ma’aikata.

An gano yadda maharan suka yi dirar mikiya da miyagun makamai misalin karfe 2:00 na rana a anguwar, inda suka doshi wajan da ake hakin tare da budewa duk wanda suka yi tozali dashi wuta.

Kwamishinan tsaro da walwalar cikin gida, Emmanuel Umar, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fita yau Alhamis, amma ya ce ba a riga an tabbatar da yawan wadanda lamarin ya ritsa dasu ba.

A cewarsa, gwamnatin jihar Neja na son tabbatar da yadda a rana 29 ga watan Yuni 2022 misalin karfe 2:00 rana suka samu kiran gaggawa kan yadda ‘yan bindiga suka yi dirar mikiya a mahakar ma’adanan da ke tsakanin kauyen Ajata da Aboki ta gundumar Erena na karamar hukumar Shiroro, inda aka shirya tawagar tsaro zuwa wajen.

Ya kara da cewa, an ruwaito yadda aka yi garkuwa da wasu ma’aikatan da ba a gano yawansu ba da ke wajen mahakar ma’adanan duk da ‘yan kasar Sin.

Ya ce an garzaya da mutane da dama da suka samu matsanantan raunuka kuma suke cikin mawuyacin hali asibitoci don neman lafiyarsu.

Sani Yusuf Kokki, daya daga cikin wadanda suka zanta da manema labarai da wasu matasan Shiroro, sun bayyanawa Daily Trust yadda aka yi garkuwa da ‘yan China da dama, inda suka siffanta lamarin a matsayin abun alhini da takaici.

Leave a Reply

%d bloggers like this: