Ministan tsaron Najeriya Bashir Magashi ya ce kusan masu laifi 600 ne su ka tsere daga gidan yari a Kuje na babban birnin tarayya Abuja.

Lamarin ya faru a daren Talata kuma ake zargin mayakan Boko Haram da kai harin.
A yayin harin an samu mutuwar jami’in hukumar kare fararen hula ta Civil Defence.

Ministan ya ce akwai kusan fursuna 300 da su ka mika kansu bayan harin ya lafa.

Hatin ya yi sanadiyyar lalata ababen hawa da wasu ɓangare na gidan yarin.
A na zargin mayaƙan Boko Haram da kai harin sai dai babu wata ƙungiya da ta dauki alhakin kai harin zuwa yanzu.