Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta tabbatar an kamo sauran mutane fiye da 300 waɗanda su ka gudu daga gidan gyaran hali na Kuje a Abuja.

Mutanen sun gudu bayan da ake zargin mayaƙan ISWAP da kai hari a daren ranar Talata.
Sama da mutane 600 ne su ka tsere daga gidan yayin da kusan 300 su ka koma da kansu a cewar gwamnatin ƙasar.

Ministan harkokin cikin gida Ra’uf regbelosa ne ya tabbatar da haka, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa a kan kafafen yaɗa labarai Sola Fasure ya sanya wa hannu.

A cewar sanarwar, tuni aka bai wa hukumomin tsaro da ke kan shingen bincike don zama cikin shirin tare da tabbatar da sa ido a kan matafiya.
Sannan an sanar da hukumomin tsaro da likitoci ko za su samu wani da ke ɗauke da raunin harbi a jikinsa.
Daga cikin mazauna gidan gyaran hali na Kuje a Abuja akwai waɗanda ake zargi ƴan ƙungiyar Boko Haram ne su 70.
Mayaƙan Boko Haram tsagen ISWAP sun kai harin ne tare da amfani da abubuwan fashewa kafin kubutar da masu laifin.
Helikwtar staro a Najeriya ta tabbatar da cewar dukkanin waɗanda ake zargi da shiga Boko Haram a gidan yarin sun tsere.
A ɓangaren guda kuwa ƙungiyar ISWAP ta ɗauki alhakin kai hari gidan yarin Kuje da ke Abuja ranar Talata.