Shugaban kasa Mahammad Buhari ya bayyana cewa ba zai gajiya ba har sai ya samar da mafita a Najeriya.

Wannan na dauke a cikin daƙon barka da sallah da ya aikewa ƴan ƙasar.
Mai magana da yawun shugaba Buhari malam Garba Shehu ne ya fitar da sanarwar a yau yayin da ake yin shugulgulan bukukuwan babbar Sallah.

Buhari ya ce ya kamata yan kasa Najeriya su Sanya kasar a cikin adduoin su bisa halin da kasar ke ciki na tsadar rayuwa da kuma rashin tsaro.

Sannan ya ce alumma bai kamata su bar koyarwar addini ba, su dinga wani abu na daban.
Mahammad Buhari ya ci gaba da cewa wadanda suke kwashe kudaden da aka tanada domin aiki ga yan kasa, wasu kuma su wawashewa zuwa aljihun su basa bin koyarwar addini.
Ya ce kudaden da za a yi amfani da su a kasa baki da daya sai mutum ya kwashe su zuwa aljihunsa kuma hakan ba daidai ba ne.
Daga karshe Buhari ya yi fatan Alhari ga musalaman kasar bisa wannan rana ta Sallah da ake ciki.