Gwamantin Jihar Zamfara ta buƙaci gwamantin tarrayya da ta sahale mata domin dawo da tsaffin ma’akatan tsaro da suka ritaya daga bakin aiki.

Gwamnan jihar Bello Matawalle shi ne ya yi rokon inda ya ce dawo da ma’aikatan tsaro wadanda suka ajiye aiki su ne wadanda za su kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.
Matawalle ya ce tsaffin ma’akatan tsaro sun San dukkanin dubarun yaki da ma yadda za a kama masu aikata miyagun laifuka, sannan ya ce hakan ne kawai zai kawo karshen matsalar a kasa.

Bello Matawalle wanda yake bayani a mahaifarsa ta Maradun ya ce yayi alkawarin mayar da Jihar Zamfara wadda ta fi kowacce jiha zaman lafiya a Najeriya

Duba ga yadda jihar Zamafara ke fuskanatar rashin tsaro, gwamnan ya sha alwashin mayar da Zamafara Jihar da ta fi kowacce jiha a Najeriya samun zaman lafiya.
Matawalle ya ci gaba da cewa yana aiki da hukumonin tsaro domin ganin an ci wannan nasarar.
Sannan ya na mai rokon gwamantin tarayya da ta karbi rokon sa na amfani da tsaffin ma’akatan tsaro masu shekaru 70 domin samun zaman lafiya a kasa.