Hukamar kiyaye hadurra a Najeriya Road Safety ta bayyana cewa mutane huɗu ne su ka mutu yayinda biyar su ka samu raunuka bayan wani hatsari da ya auku a jihar Legas.

Shugaban hukumar kiyaye hadurra ta kasa shiyyar jihar Legas Ahmad Umar shine ya bayyana haka ga manema labarai a yau a Abekuta.

Umar ya ce hadarin ya faru a jiya Litinin akan babbar hanyar Toll gate Ogere zuwa Ibadan.

Ya ce hadarin ya auku sakamakon wani mai motar siyana da motar ta kubuce masa su ka hadu da wata babbar motar daukar kaya.

Ahmad Umar ya ce mutane Tara ne hadarin ya rutsa da su Hudu sun rigamu gidan gaskiya yayin da biyar su ka samu raunuka.

Daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su akwai maza shida da mata da kuma Yaro karami.

Sannan an kai wadanda su ka samu raunuka babban asibitin Ogere domin kulawa yayin da aka mikawa iyalan wadanda su ka rasu gawarwaki domin jana’iza.

Daga karshe ya shawarci alumma da su daina yin gudun wuce sa’a a kan tituna musamman ma likacin damina.

Leave a Reply

%d bloggers like this: