Shugaban kasa Mahammadu Buhari ya yi kira ga kungiyar malaman makarantar Jami’a ta Najeriya wato ASUU da ta janye yajin aikin da suke yi.
Buhari ya buƙaci haka ne a jiya lokacin da gwamnonin kasar da kuma manyan jiga_jigan jamiyar APC su ka kai masa ziyara Daura a Katsina.
Buhari ya ce ya kamata kungiyar malaman makaranta ta ASUU ta dubi halin da dalibai ke ciki a kasar su janye yajin aiki.
Hakan ya na ƙunshe cikin jawabin da mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu ya fitar.
Buhari ya ce yajin aikin da malaman makaranta su ke yi yayi matukar yawa sannan ya damu gwamanti da ma iyayen daliban.
Ya ce dukkan ci gaban kasa yana tare da ilimin yan kasar yakamata ASUU ta koma ta ci gaba da koyar da karatu a Makaranta.
Shugaban ya ci gaba da cewa ya san ƙungiyar ASUU za ta tausayawa ɗalibai bisa halin da su ke ciki na tsawon watanni Biyar a gida ba tare da Karatu ba.