Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya musanta rade-radin da ake yi na cewa ya rubuta takardar fita daga jam’iyyar APC.

Farfesa Yemi Osinbajo ya musanta raɗe-raɗin bayan da ake zargin zai fice daga jam’iyyar APC.

Ana jita-jitar Farfesa Yemi Osinbajo ya aikawa Muhammadu Buhari takarda yana neman sauya-sheka, saboda APC ta ba Musulmi da Musulmi takara.

A cikin takarda mai lamba SH/VP/605/2./0 da ake yadawa, ana ikirarin Osinbajo ya bayar da dalilan da suka sa zai bar APC, har da matsin lamba daga rigimar cikin gida.

Haka zalika takardar ta nuna mataimakin shugaban kasa ya gaji da cigaba da shiga harkar siyasa.

Jaridar Daily Trust ta nemi jin ta bakin Mai magana da yawun mataimakin shugaban Najeriyan, Laolu Akande a game da takarda aka fitar.

Laolu Akande ya tabbatar da cewa babu gaskiya a wannan batu, ya ce takardar ta boge ce.

Hadimin fadar shugaban kasar ya ce idan aka duba rubutun, za a fahimci ya sha bambam da na Farfesa Osinbajo, sannan cike takardar take da kura-kurai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: