Wasu da ake zargin yan bindinga ne sun hallaka mutane bakwai wadanda suke dawowa daga daurin aure a jihar Imo.

Lamarin ya faru a daren Lahadi akan babbar hanyar kauyen Otulu da ke karamar hukumar. Oru ta jihar Imo.

Rahotanni sun bayyna cewa wata gayyar zuwa daurin aure da ta biyo hanyar Otulu yan bindigan sun bude mata wuta tare da hallaka mutane Bakwai nan take.

Shugaban kauyen Otulu Nmamdi Agbor ya tabbatarwa yan jarida cewa an kashe mutane bakwai yayin da aka tarwasta sauran.

Agbor ya ce wadanda lamarin ya faru da su sun koma ne daga daurin auren gargajiya daga Awo Omamma inda yan bindidga su ka bude musu wuta.

Sannnan ya ce yanzu haka sun samu gawarwaki biyar wasu kuma sun samu raunuka kuma ba a ga biyar daga ciki ba .

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Mecheal ya tabbatar da faruwar lamarin sannan ya ce za su tabbatar an kma mutanen da su ka yi wannan aiki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: