Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC tabayyana cewa a zaben shekarar 2023 mai zuwa mawuyaci ne mazauna gidajen gyaran hali da ke fadin Najeriya su jefa kuri’a a zaben.

Shugaban Hukumar ta INEC Muhammad Yakubu shi ne ya tabbatar da hakan a ya yin ziyarar da hukumar da ke kula da gidajen yari a Najeriya ta kai masa a Ofishinsa da ke birnin tarayya Abuja a jiya Talata.

Shugaban hukumar ta INEC ya ce sai an cimma matsaya daya sannan mazauna gidajen yarin za su jefa kuri’un nasu.

Muhammad Yakub ya kara da cewa watanni bakwai kadai su ka rage a fara gudanar da zaben,inda ya ce dole a sanya ido wajen samun hanyoyin da mazauna gidajen yarin za su kad’a kuri’un.

Shugaban ya ce ba zaben shekarar 2023 mai zuwa ba shi ne zaben da Najeriya ta daina gudanar da zabe ba akwai sauran zabe da za a yi a nan gaba.

Farfesa Muhammad Yakub ya ce ko da hakan bai yuwu gaba daya ba na bai wa “yan gidan yarin izinin yin zaben a zaben shekarar 2023 za su ci gaba da yin duba akan hakan har zuwa zabe na gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: