Rundunar “yan sandan Jihar Jigawa ta kama wani mai shekara 33 mai suna Mahdi Salisu wanda ake zargi da dillancin kayan maye a Jihar.

Rundunar ta kama Mahdin ne a cikin karamar hukumar Taura ta Jihar.

Kakakin rundunar “yan sandan Jihar Lawan Shisu Adam shine ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike ga manema labarai a garin Dutse na Jihar.

Lawan Shisu ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a lokacin da jami’an na ƴan sandan su ka samu bayanan sirri a kan matashin.

Jami’an “yan sandan sun kama Mahdi ne a lokacin da su ka samu bayanan sirri daga cikin karamar hukumar ta Taura cewa an ganshi dauke da kunshin tabar wiwi Guda dari da biyu da kuma wata a cikin bakar leda.

Kakakin ya ce bayan kamashi an gano wasu da su ke taimaka masa wajen safarar kayan maye.

Lawan Shisu Adamu ya kara da cewa bayan sun kammala bincike za su gurfanar da su a gaban kotu domin yi musu hukuncin.

Kwamishinan “yan sandan Jihar Aliyu Sale Tafida ya bayar izinin ga dukkan baturen yan sanda na kowane yanki da su dinga kai sumame maboyar masu aikata laifuka a mako sau biyu a Jihar.

Sannan Kwamishinan ya kuma yi kira ga masu aikata laifuka a Jihar da su daina tun kafin su shiga komar su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: