Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na tunkarar kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta, yana mai cewa ba zai bar wata kafa ba wajen murkushe ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda da ke barna a sassan kasar.

Shugaban kasar a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi, ya ce an ci gaba da matsawa hafsoshin tsaro don ganin an magance matsalar ‘yan fashi da ta’addanci.
Ya kuma jajanta wa tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Adamu Muazu, kan kisan dan uwansa da wasu ‘yan bindiga suka yi.

Da yake bayyana ‘yan bindigar a matsayin makiyan mutane, Buhari ya ce ya kadu da mummunan kisan da aka yi wa wanda aka kashe.

Ya yi addu’ar Allah ya jikan mamacin ya kuma baiwa iyalai haƙuri tare da tabbatar da cewar za a ɗauki kataki.
Bayanin Shugaban na zuwa ne sa’o’i bayan da ‘yan ta’addan suka fitar da wani faifan bidiyo inda suke dukan wadanda harin da aka kai kan wani jirgin kasa da ke kan hanyar Kaduna a ranar 28 ga Maris.
Maharan sun sha alwashin ci gaba da kai hare-hare tare da barazanar kai wa manyan shugabannin kasar hari.