Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya sha alwaahin goyon baya wajen kawo karshen yajin aikin ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ASUU.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da shugabannin ƙungiyar kwadago NLC reshen jihar Kano su ka ziyarceshi a yayin gudanar da zanga-zangar lumana don jan hankalin gwamnati a kan lamarin.

Malaman jami’a a Najeriya sun shafe fiye da watanni biyar su na yajin aiki wanda hakan ya kawo tsaiko a karatun ɗaliban makarantun.

Ƙungiyar ƙwadago ta ɗauki matakin zanga-zangar lumana a ƙasar domin nuna rashin goyon bayan kawo karshen yajin aikin.

Shugaban ƙungiyar ƙwadago a Najeriya Kwamared Ado Minjibir ya jinjinawa gwamnan Kano wajen ganin ya ci gaba da biyan malaman jami’a duk da cewar su na yajin aiki.

Ƙungiyar kwadagon da sauran ƙungiyoyin ɗalibai sun shiga zanga-zangar a yayin da su ka ziyarci fadar gwamnatin Kano a yau Talata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: