Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki zagon kasa (EFCC), sun kama wasu mutane 13 da ake zargi da damfarar yanar gizo.

An damke mutanen ne da sanyin safiyar ranar Alhamis 28 ga watan Yuli, 2022, a wani sumame da aka kai a wurare daban-daban a garin Fatakwal a jihar Ribas.
Kamen nasu ya biyo bayan bayanan sirri da hukumar ta samu kan zarginsu da hannu a zamba ta intanet.

Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da motoci, wayoyin hannu iri daban-daban, Katin cirar kuɗi na ATM da na’ura mai kwaƙwalwa ta tafi da gidanga watoLaptop.

Haka zalika, jami’an hukumar EFCC shiyyar Fatakwal a ranar 21 ga watan Yuli, sun kama mutane saba’in da hudu (74) da ake zargi da damfarar yanar gizo.
An kamesu ne a wurare daban-daban a Fatakwal, Jihar Ribas.