Connect with us

Labarai

Faɗuwar Darajar Naira – EFCC Sun Dira Kasuwa Chanji Ta Abuja

Published

on

Jami’an Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC sun yi dirar mikiya a kasuwar chanji ta Zone 4 a birnin tarayya Abuja domin kama wadanda su ka boye dala.

Jami’an su kai sumamen ne sakamakon wasu “yan kasuwar da su ke boye dalar Amuruka wanda hakan ke sanyawa farashin kayayyaki ya ke tashi a Najeriya.

Jami’an sun ce yin hakan da “yan kasuwar su ka yi ya haddasa faduwar naira a kwanakinna.

Ba tun yanzu ba jami’an sun dade su na sanya idanu akan yan kasuwar ta chanji dala wanda su ke boyewa daga bisani su fitar da ita kasashen ketare.

Bayan zuwa kasuwar yan chanjin da jami’an na EFCC su ka yi hukumar ta sake aike da jami’an ta Filayen Jiragen sama na Jihar Kano da Legas da kuma garin Part Horcort domin damke masu shirin fita da dalar kasahen ketare.

Hukumar ta EFCC ta tura jami’an ne sakamakon faduwar farashin Naira da aka yi a Jiya Alhamis wanda ba a taba samu ba, yayin da ita kuma dala daya ta kai Naira 705 a kasuwar chanji.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Fasinjoji Biyu Sun Mutu Sakamakon Ruftawar Gada A Ebonyi

Published

on

Rundunar ƴan sanda a jihar Ebonyi sun tabbatar da mutuwar wasu fasinjoji biyu sanadin ruftawar wata gada a jihar.

Mai magana da yawun ƴan sanda a jihar Joshua Ukandu ne ya tabbatar da haka a Abakaliki yau Litinin.

Ya ce lamarin ya faru da misakin ƙarfe 10:00am na safiyar yau a ƙauyen Mgbabeluzor da ke ƙaramar hukumar Izzi a jihar.

Ya ce tuni aka kai gawar mutanen babban asibitin Iboko sashen ajiye gawarwaki.

Gadar wadda ake gyaranta ta rufta yayin da ma’aikatan ke kusa da ita.

Sannan mutanen biyu sun mutu ne sakamakon munanan rauni da su ka samu.

 

 

 

 

Continue Reading

Labarai

Gwamnan Edo Ya Amince Da Dubu 70 Matsayin Mafi Karancin Albashi

Published

on

Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya amince da dara biyan ma’aikatan jihar mafi ƙarancin albashi naira 70,000.

Obaseki ya bayyana haka yau Litinin yayin ƙaddamar da gidan ma’aikata.

Ya ce zai fara biyan mafi karancin albashin daga watan Mayu mai kamawa.

Batun ƙarin albashi na daga cikin dalilai da ya sa kungiyoyin kwadago a Najeriya ke yin zanga-zanga wanda su ka buƙaci a ƙarawa ma’aikata a kowanne mataki.

A baya ƙungiyar ta bukaci a mayar da mafi ƙarancin albashin naira 30,000, sai sai sun bukaci ƙari bayan da aka cire tallafin mai a shekarar 2023.

Sai dai wasu gwamnonin sun nuna ƙin amincewa da haka a baya.

 

 

 

 

Continue Reading

Labarai

Kotu Ta Sanya Ranar Da Za Ta Yankewa Ganduje Hukunci Kan Zargin Rashawa

Published

on

Babbar kotun jihar Kano ta tsayar da ranar yanke hukunci dangane da zargin tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje bisa karɓar rashawa.

 

Kotun ƙarƙashin mai shari’a Usman Malam Na’abba, ta tsayar da ranar 16 ga watan Mayu a matsayin ranar da za ta yanke hukuncin bayan sauraron kowanne bangare.

 

An shigar da ƙarar tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da matasar da ɗansa kan zargi takwas wanda ciki akwai cin hanci, karkatar da kudaɗe da sauransu.

 

Baya ga tsohon gwaman, akwai wani kamfani da aka shigar da ƙarar wanda yana daga cikin waɗanda ake ƙara.

 

Gwamnatin Kano ce ta gurfanar da su a gaban kotu, tare da gabatarwa da kotu shaidu 15 a kan zargin da take musu.

 

Bayan sauraron ɓangaren masu ƙara da waɗanda ake ƙara, kotun ta tsayar da ranar 16 ga watan Mayu domin yanke hukunci a kai.

 

 

 

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: