Wannan shafi da ke kawo muku rahoto na musamman a ciki, a wannan watan ma muna ɗauke da wani rahoto wanda  zai mai da hankali kan yadda  ake gudanar da auratayya ba tare da gwajin jini ba,  duk da irin kiraye kirayen da        jami’an lafiya ke ta ya kan a dinga gwajin jini kafin aure.

A baya dai iyaye da kakanni basu san wani abu ba wai shi gwajin jini kafin aure ba, sun kasance suna yin aure ne bisa tafarkin biyayyar iyaye ko kuma soyayya a tsakanin junansu.

Sai gashi a yanzu ana ta gudanar da maƙaloli da kuma gangami, har da kiraye kiraye a masallatai kan a dinga gwajin jini kafin aure, duk da ba     kasafai ake amsa kiraye kirayen ba kasancewar Al’umma na tsoron zuwa a gwada jininsu don gudun haifar musu da matsala akan neman auren da suke.

Wannan gwajin jini da ake ta kiraye kiraye aje ayi ba lallai sai gwajin HIV Ba ana zuwa gwaji don sanin matsayin jinin halittarka, saboda sanin wa ya dace ka aura wacce zaku dinga haifan ƴaƴa lafiyayyu  ba tare da wasu ƙwayoyin cututtukan da zai dinga wahalar dasu .

Sai dai wani abin da ke wahalar da masoya a     wannan lokaci shine sai bayan sun shaƙu da juna wata ƙila sai ana dab da yin auren su, sai ace suje su gwada jini don gudun faɗawa matsala, wanda daga ƙarshe idan aka samu sakamakon da bai yi musu daɗi ba sai ya zama sun shiga wani yanayi na rashin son rabuwa da juna.

Kamar yadda ta faru da wasu masoya, Suleman da Maryam suna son junansu anyi maganar aure, sai iyaye suka bada shawara akan suje su gwada jininsu, da aka bincika sai sakamako ya nuna cewa  Suleman da Maryam suna ajin AS ne wato akwai yaƙinin zasu iya haifar ƴaƴa masu dauke da cutar Sikila (sickler).

Wanda kamata yayi ace AS ya auri AA, ko kuma mai SS Ya auri AA, shine za’a dinga haifar            lafiyayyun ƴaƴa.

A yanzu  haka dai sun kasa rabuwa da juna kasancewar sun shaƙu sosai suna ganin idan suka rabu ba lallai ita ta samu wanda take so ba, haka shima abin da yake tunani kenan, wannan shine abin dake  haifar da matsala akan gwajin jini kafin aure.

Haka zalika Mujallar Matashiya taji ta bakin wasu matasa inda wani matashi Abubakar mai laƙabin Ɗan Beauty  ya bayyana cewa shi bazai iya haƙura da yarinyar da yake so ba, idan har aka gano cewa jininshi da nata ka iya haifar da matsala idan suka yi aure ta hanyar Haifar ƴaƴa marasa lafiya.

A cewar ɗan Beauty shi so wani abu ne wanda idan aka fara shi to babu rabuwa sai dai mutuwa ta raba, amma cuta ko wani abu bazai sa ya ja     baya ba kan soyayyarsa.

Ita kuwa Aisha Humaira ta bayyana cewa ita zata iya rabuwa da saurayinta muddin aka gwada jininta aka tabbatar zasu iya jefa ƴaƴansu cikin wani yanayi, to gwanda su hakura Allah ya haɗa kowa da rabonsa.

Ta ƙara da cewa ana aure ne don raya sunna tare da haifar ƴaƴan da zasu taimakeka, to idan ka   haifi ƴaƴa ba lafiya kenan zaku kasance ne kullum cikin ɗawainiyar zuwa asibiti, wanda ba haka aka so ba, gwanda tun farko a magance matsalar tun kafin a shiga.

Shima wani ƙwararran likita mai zaman kansa Dr Ibrahim mohammad ya bayyana cewa gwajin jini abu ne mai kyau musamman ga masu shirin aure don gudun faɗawa matsala ta hanyar haifar ƴaƴa marasa cikakken lafiya.

Haka zalika gwajin HIV shima abu ne da ya dace masu shirin aure su dinga yi, amma dai sanin matakin rukunin da jininka yake abu ne da ya dace don gano macen da zaka aura, haka ita ma ta gano irin mijin da zata aura bayan an bincika halayensa na nagari da mu’amalarsa a cewar Dr Ibrahim.

Ga yadda rukunin jini yake da kuma yadda masu son yin aure  ya kamata su kasance.

AA+SS = Yayi dai dai

AA+AA= Yayi dai dai

AA+AS= Ba damuwa

AS+AS= Bai yi ba

AS+SS = Da matsala

SS+SS= bai yi ba kwata kwata.

Wannan sune na’uikan ajujuwan jinin mutane da yadda ya kamata su auri juna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: