Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutun ma’aikatan gwamnati a Jihar bisa shigowar sabuwar shekarar Musulunci.

Tambuwal ya bayyana hakan ne a jiya juma’a a yayin wata ganawa da yayi da sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar Na uku.

Gwamna Tambuwal ya Bukaci al’ummar Jihar da su dage wajen yin addu’o’i na samun zaman lafiya da kuma shugabanci nagari a lokacin da su ke gudanar da hutun.

Aminu Waziri Tambuwal ya kara da cewa hakan ya na da matukar muhimmaci bisa koyarwar addinin musulunci domin watan ya na daya daga cikin watanni hudu masu alfarma.

Tambuwal ya ce a guji aikata manyan laifuka a watan ,sannan kuma yayi addu’ar samun gafara da rahma a sabuwar shekarar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: