Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Abiodun Alabi, ya baiwa mazauna jihar tabbacin samun isasshen tsaro biyo bayan rahotannin da ke nuni da cewa jihar na cikin jerin jihohin da aka shirya kai wa hari a fadin kasar.

Alabi ya bayar da wannan tabbacin ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya fitar.

Ya ce, rundunar ta kama aiki kafada da kafada da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da cewa babu wani mutum ko gungun jama’a da za su yi nasarar dakile zaman lafiya da kwanciyar hankali da mutanen jihar Legas ke da shi.

Tun da farko, Hundeyin, a wani shafin yanar gizo na Twitter Space, a ranar Asabar, ya amsa tambayoyi daga jaridar The PUNCH, game da rahotannin yiwuwar harin da ‘yan ta’adda suka shirya kaiwa Legas, da kuma shirye-shiryen ‘yan sanda, inda ya lura cewa ‘yan sanda suna samun rahotannin sirri.

Hundeyin ya ce, suna aiki da gaske tare da sauran hukumomin tsaro, Sau da yawa yana tare da kwamishinan ‘yan sanda, Abiodun Alabi, ma’aikatar harkokin gwamnati ta kan aika musu da rahoton sirri.

Ya ce mazauna Legas suna bukatar su taimaka wa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro wajen samar musu da bayanan da suka dace a kan abubuwan da ake zargi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: