Akalla mutane bakwai ne wasu ‘yan bindiga suka kashe a karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato.

Kisan na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan wasu mutane 18 suka rasa rayukansu a wani rikici tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan banga a yankin karamar hukumar Wase da ke jihar.

Sakataren yada labaran kungiyar Berom Youth Mooulders Association, Rwang Tengwong, ya tabbatar da kashe-kashen baya-bayan nan a karamar hukumar Jos ta Kudu a Jos a yau Litinin.

Tengwong ya ce, an tabbatar da mutuwar mutane bakwai a yankin Danda chugwi bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kai.

Harin ya faru ne a ranar Lahadi 31/07/2022 da misalin karfe 9:00 na dare.

Wasu da suka samu munanan raunukan bindiga an kai su asibitin Vom Christian domin kula da lafiyarsu cikin gaggawa.

Hukumomin tsaro a jihar da suka hada da ‘yan sanda da rundunar soji ta musamman da ke kula da zaman lafiya ba su fitar da wata sanarwa ga jama’a dangane da kashe-kashen ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.

Leave a Reply

%d bloggers like this: