Mazauna garin Abeokuta a Jihar Ogun na zaman ɗar-ɗar bayan kama wani da ake zargin shugaban kungiyar Boko Haram ne.

Hukumar yan sandan farin kaya tabDSS, ce ta kama wanda ake zargin.
Wata majiya kwakwara ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa an kama wanda ake zargi shugaban ne a Boko Haram a unguwar Ijaye a Abeokuta.

Majiyar ta ce da farko wanda ake zargin ya nuna tirjiyya amma daga bisani DSS ta yi galaba a kansa.

An kama shi ne a cikin dare, majiyar ta shaida wa Daily Trust a daren ranar Lahadi.
Majiya daga hukumar tsaro ta ce ya tafi Abeokuta ne domin kafa sansani na garkuwa da mutane da kai hare-hare.
Hakan na zuwa ne a lokacin da ake zargin yan ta’adda na shirin kai hari a wasu jihohin kudu maso yamma.
Da aka tuntubi Kakakin DSS, Dr Peter Afunanya, bai tabbatar da kamen ba kuma bai musanta kamen ba.