Rundunar ƴan sandan jiar Neja sun samu nasarar kama masu garkuwa da mutane mutum biyu a jihar.

An kama Usman Rabi’u mai shekara 22 da Nafi’u Umar mai shekara 18 a ƙramar hukumar Tafa bayan zargin yin garkuwa da wani Yasir Salisu a ƙarshen watan day a gabata.
Yarin Salisu da aka yi garkuwa das hi mai shekaru 13 a duniya an shiogar da ƙorafin garkuwa da shi a ranar 29 ga watan Yulin day a gabata.

Mai Magana da yawun ƴan sandan jihar Wasiu Abiodun ne ya tabbatar da kama matasan biyu a ƙaramar hukumar Tafa ta jihar Neja.

Sai dai ƴan sandan sun ce an hallaka Yasir Salisu da aka yi garkuwa dashi sannan aka binne shi a cikin ƙaramin rami.
Matasan dasu ka yi garkuwa das hi sun buƙaci a basu kuɗin fansa naifra 100,000 kafin sakinsa, sai dai daga bisani aka gano sun hallaka mamacin.
A wani labarin kuma ƴan sanda a Neja sun kama wani John Ijamu daya tsere daga gidan yari na Kuje a babban binrin tarayya Abuja
An sake kama John a Minna babban birnin jihar ranar 28 ga watan Yulin day a gabata.
Wanda aka sake kamawa an kaishi gidan yarin ne bayan kamashi da aikata fashi da makami a shekarar 2020.