Hukumar kula da sufurin jiragen kasa a Najeriya NRC ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa daga Kano zuwa Legas zuwa Ajakuta ranar Talata.

Shugaban hukumar Fidet Okhiria ne ya tabbatar da hakan a ranar Talata wanda ya ce hakan ya biyo bayan wani hari da aka kai wa fasinjojin a ranar Litinin.

Matakin hakan ya biyo bayan rahotannin tsaro da aka samu a kan yunkurin kai wa jirgin hari.

Wasu rahotanni sun tabbatar da cewar an kai wa wasu fasinjojin jirgin ƙasan a ranar Litinin.

Hukumar NRC ta ce a halin da ake ciki ana fuskantar matsalar tsaro a jihohin Kaduna, Neja da sauransu.

Hukumar ta ce ba ta tsayar da lokacin da za a dawo jigilar fasinjojin ba har sai komai ya daidaita.

Leave a Reply

%d bloggers like this: